Gwamnatin Kwankwaso ce ta lalata ilimi a jihar Kano – Inji Musa Iliyasu

Kwamishinan raya karkara na jihar Kano Alh. Musa Iliyasu Kwankwaso, ya yi ikirarin cewa tsohuwar gwamnatin Rabi’u Musa Kwankwaso ce ta lalata ilimi a jihar Kano.

Musa Iliyasu kwankwaso ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke hira da gidan rediyon Freedom da ke Kano, inda ya ce duk wani tsarin ilimi a jihar Kwankwasiyya ce ta lalata shi, kuma babu wata jami’a da Kwankwaso ya gina domin jihar Kano tana da tsarin ci gaban iliminta tun asali.

Haka kuma Musa Iliyasu Kwankwaso ya yi zargin cewa dattawan Kano da su ka gurfanar da gwamna Abdullahi Umar Ganduje a gaban shugaba Buhari akan ciyo bashi daga ƙasar China, domin yin layin Dogo a jihar Kano, ya ce ba dattawan Kano bane dattawan Kwankwasiyya ne, A makon jiya ne wata gamayyar ƙungiyoyi da ke rajin kare mutuncin mutanen Kano ta kai ƙarar Gwamnan jihar Abdullahi Ganduje ga shugaba Muhammadu Buhari kan yunƙurinsa na ciyo bashi daga wani bankin China domin gina hanyar jirgin ƙasa.

Gamayyar ƙungiyoyi fiye da 15 ƙarƙashin inuwar Kano Forum ta bayyana abin da ta kira katafaren bashin da gwamnatin Ganduje ke son karɓowa domin gina kashin farko na hanyar jirgin ƙasa a birnin Kano a matsayin abin da ba shi da amfani ganin manyan kalubalen da ke gabanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published.