Daga Yanzu sai karfe 11 na dare Babura zasu daina yawo—inji Gwamnatin Katsina

Gwamnatin Jahar Katsina ta sassauta dokar Zurga-zurgar Babura daga Karfe Shidda na Safe zuwa Sha daya na daren kowacce rana

Wannan na Kunshe ne a cikin wata takarda da Kwamishinan yada Labarai, Al’adu da Al’amurran cikin gida Alhaji Abdulkarim Yahay Sirika ya fitar aka rarrabawa manema labaru a Katsina

Takardar ta bayyana cewa sassauta lokacin dokar yanzu ya shafe dokar dake aiki a baya, wacce take farawa daga shidda na Safe zuwa Bakwai na dare.

Kwamishinan yayi kira ga masu amfani da Babura dasu bi dokar yanda ya dace gami da cigaba da zama yan Kasa nagari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *