Gwamna Ganduje Ya Kai Ziyara Wurin Aikin Samar Da Wutar Lantarki Da Gwamnatinsa Ke Yi

 

Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR da Mataimakin sa Dr Nasiru Yusuf Gawuna sun duba aikin wutar lantarki mai aiki da karfin ruwa wanda gwamnatin sa ke yi a dam din Tiga da Challawa mai karfin wutar lantarki Megawatts 15, inda dam din Tiga zai samar da 7.2 Megawatts sannan na challawa kuma zai samar da sauran.

Haka kuma Gwamna Ganduje ya duba wurin tattara wutar wato substation a Challawa da kuma aikim kwashe wutar daga Tiga zuwa wajen tattara wutar na Challawa.

Idan an kammala aikin wutar, za’ai amfani da ita a gidajen matatar ruwa na jiha da kuma wutar kan titi wato streetlight inda zaa daina amfani da janareto.

Aikin Tiga dam din a yanzu yana kashi 95% ne, kuma ana karasa aikin wanda zaa hada bututun da ruwan zai shiga domin samar da wurin da kuma dam din inda ruwan zai fito.

Akwai buturu guda biyu wanda daya idan ya samar da wutar zai wuce zuwa kogin Kano wato River Kano, sannan dayan kuma zai shiga gonaki domin noman rani. Zaa kammala aikin gaba daya nan da wata daya kafin a fara aikin gwaji na wutar.

Gwamna Ganduje na tare da Alhaji Nasiru Aliko Koki DG Campaign din Ganduje, da Kwamishinoni da masu bawa gwamna shawara da sauran manyan jamian gwamnatin jiha.

Leave a Reply

Your email address will not be published.