Bude Makarantu Yanzu Ba Karamin Ganganci Ba Ne, Cewar ASUU

Kungiyar malaman jami’a ta Nijeriya, ASUU ta ja kunnen gwamnati cewa bude makarantu ba tare da wani tanadi na hana yaduwar cutar Corona virus ba, ba karamin ganganci bane.

ASUU tace idan gwamnatin ta ki ji ta yi gaba gadi wajan bide makarantun to duk abinda ya faru ta kuka da kanta.

Reshen kungiyar na jihar Legas ne ta bayyana haka.

Memban kungiyar, Farfesa Olusiji Sowande ne ya bayyana haka a ganawar da yayi da manema labarai.

Yace babu tsarin da za’a yi nesa-nesa da juna a dakunan kwananan dalibai hakanan babu wannan tsari a ajujuwa.

Ya kara da cewa yawancin makarantun babu isashshen ruwa da za’a kula da tsafta da dai sauran matakai da ya kamata a dauka dan haka yace jami’o’in basu shirya ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.