Kungiyar kwato wa talaka hakkokin su da tabbatar da adalci (SERAP) ta maka Shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari a babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Abuja.
SERAP ta maka shugaban kasar ne saboda ya gaza bayyana sunayen mutanen da gwamnati tace ta kwato Naira Biliyan 800 (N800bn) daga wajensu, da kuma ayyukan da aka yi da kudaden.
Sanarwar shigar da karar Shugaba Buhari a Kotun na dauke da sa hannun Mukadashin Shugaban Kungiyar SERAP Kolawole Oluwadare wanda ya ce suna neman kotu ta umurci Shugaba Buhari ya wallafa sunayen mutanen da aka kwato kudaden daga wajensu, sanan kuma a wallafa ranaku da wuraren da aka yi ayyuka da kuma irin ayyukan da aka yi.
Kungiyar ta kuma bukaci bayani daga Ministan shari’a na kasa Abubakar Malami, da kuma Ministar kudi Zainab Ahmed.
Kungiyar ta bayyana cewa kasancewar Najeriya daya daga cikin kasashen da suka sa hannu a taron Majalisar Dinkin Duniya kan yaki da cin hanci da rashawa haki ya taraya a wuyanta na tabbatar da ganin ana bin wannan doka sau da kafa a cikin kasar.
Wani abu da ya dauki hankali a karar shi ne yadda kotu ta umurci Shugaba Buhari ya tilasta wa hukumomin yaki da cin hanci da rashawa irin su ICPC da EFCC su yi hanzari su binciki yadda aka raba wasu kudade har biliyan 51 daga asusun gwamnati a shekara 2019.
SERAP tace ta shigar da karar ne domin yan Najeriya na da yancin sanin yadda ake aiwatar da kudaden kasa domin samun fahimta da kara yarda tsakanin gwamnati da al’umar da ta ke mulka inda tace saboda haka ya zama wajibi Gwamnati ta fito dan fadawa yan kasa inda aka kwana kan kudaden da aka kwato.