Aikin Laying Dogo Na Nan Daram A Kano, Dattawan Kwankwasiyya Ne Suka Kai Karata Wajen Buhari – A cewar Ganduje

Gwamnatin jihar Kano Karkashin Jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta shaidawa dattijan Kwankwasiyya cewar babu gudu babu ja da baya game da kokarin da take yi na ranto kudade domin gina layin dogo a jihar.

Kwamishinan Yada Labarai na Kano Muhammad Garba. Yayin da yake mayar da martani ga dattawan Kwankwasiyya. Ya ce mun tattauna da duk masu ruwa da tsaki a jihar Kano kafin daukar mataki.

Ya ce babu wani dan adawa da zai tilasta musu yin murabus a kokarinsu na maida Kano babban birni.

Baya ga sauran fa’idodi, aikin layin zai bunkasa kasuwanci, da sauƙaƙa safarar kayayyakin amfanin gona daga dukkan sassan jihar.

Ya kara da cewa tunda Bankin Shige da Fice na kasar Sin ya riga ya amince da bukatar ba da rancen, gwamnatin ba ta da zabi illa ta cire kudaden don wannan aikin.

Muhammad Garba ya ce gwamnatin jihar ta dauki dukkan matakan da suka dace don karbo bashin, samun amincewar majalisar dokokin jihar da dukkanin hukumomin gwamnatin tarayya da suka dace.

Kwamishina ya ce duk da cewa bai yi mamakin matakin Kwankwasiyya ba, duba da cewa basu taba yaba wa duk wani mataki da gwamnatin APC ta dauka wanda ta kuduri aniyar aiwatar wa ba, komai kyan abun su a gurin su ba mai kyau bane.

Leave a Reply

Your email address will not be published.