#RanarHausa: Kayayyaki na ajiya wanda ake sakawa da KABA ko da FATA A Garin Hausa

RANAR HAUSA TA DUNIYA

A ƙasar Hausa, shekaru da dama da suka wuce musamman wanda suka yi zama na ƙauyuka za kaga ana samun kayayyaki na ajiya wanda ake sakawa da KABA ko da FATA aka yisu. Wanda waɗannan kayayyaki suke taimakawa Bahaushe ajiyar kayansa. A cikinsu akwai:

Waɗanda ake yi da fata:

Tailki

1. TAIKI: anayin shi ne da fata watau Buhu da aka ɗinka da fata akai masa ƙofa a tsakiya don zuba hatsi. Har Bahaushe yakan ce anbar dukan jaki an koma dukan taiki.

 

SULKUMI

2. SULKUMI: Babbar jaka ce da akayi da cikakkiyar fatar akuya/rago akai mata ƙaramin baki. Akan ce mata Asurkumi.

 

TANDU

3. TANDU: Wani irin makai mai kama da sintali da ake yi da ƙirgi musamman don saka man shanu ko wani abu dake da alaƙa da mai a ƙasar Hausa. Shi Tandu yana kama da sintali. Sintali shine butar ƙarfe ko ta ƙasa. Harma akan ba mai riƙe da wannan buta a masarauta da sarautar Shantali. Wanda ake zuba kwalli shi ake kira da KURA-TANDU wanda ake yin shi da fata. Har Bahaushe yakan ce sai dai kwaɗayi ya kashe ni amma ba zanci kura-tandu ba. Mashiyi shine abinda ake sa kwalli ɗin. Akwai na ƙarfe akwai na fata.

 

GAFAKA

4. GAFAKA: Jakar fata ce da ake saka Al-Qur’ani ko wasu littattafai na ilimi. Dukawa ne suke ɗinka gafaka.

 

ZABIRA

5. ZABIRA: Jakar fata ce wanda wanzamai ke zuba kayan Asaki watau askoki da kayan aski, d.s.s wasu sukan kirata da TAMPOLO.

 

6. BURGAMI: Jaka ce ta fatar akuya, mata sukan ɗauke ta su rataya da makamantansu.

BURGAMI

7. SALKA: Anayin ta da fatar dabba watau cikakkiyar fatar dabba don zuba ruwa a wajen tafiya musamman adā da ake tafiyar ƙafa ko kuma akan raƙuma.

Har Bahaushe yakan ce wai Daji yaci mai Salka bare mai Gyanɗama (ƴar gora). Har Bahaushe yakan ce ana neman ruwa a jallo.

Jallo gora ce ƴar ƙarama ana cema ta jallo,gora, Gyanɗama. Dalilin da yasa ake wannan Karin Maganar saboda duk wanda yake tafiya a Sahara zaka ga babban abinda yake nema shine ruwa, saboda ƙishin ruwa buƙatarsa ya sami ruwa. Idan kana neman matuƙar abu iyakar matuƙa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: