Za’a Fara Yiwa Mata Gwajin Shan Miyagun Kwayoyi Kafun Aure A Maiduguri-Hukumar NDLEA

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi reshen jihar Borno ta bukaci a fara gwajin shan miyagun kwayoyi wa matan da Za’a aurar domin tabbatar da hankalin su.

Shugaban hukumar ta NDLEA reshen Borno Mohammed Mustapha Abdallah shi yayi wannan tsokaci duba ga yawaitar karuwar shan miyagun kwayoyi a tsakanin ƴan mata da matan aure a jihar.

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewar shugaban ya bukaci Limamai da fastoti da su sanya wannan doka cikin dokokin daurin aure a masallatai da cocunan jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published.