Yadda Aka Kashe Direba Ja’afar Manga A Jihar Imo

Wannan labari da ban tausayi yake.

Jami’an tsaro sun kai ga gano gawar Jafaru Manga a cikin wata gona bayan an daure shi an yi masa kisan gilla a garin Owerri dake jihar Imo.

Abinda ya faru shine-:

Shi Ja’afaru Manga ya dauko fasinja ne daga jihar Ilori zuwa jihar Gombe bayan sun isa Gombe suka karbi lambar wayar sa lokacin da za su koma sai suka nemi ya maida su kuma lokacin washegarin Sallah sai ya ki, sai suka bayyana masa cewa sun ji dadin tukin sa ne kuma za su dauki shata ne ba sai ya nemi karin fasinja ba. Sai ya amince zai maida su.

Tunda ya tafi ba a sake jin duriyar sa ba, wayar sa ko an kira ba ta shiga tunda suka tafi. Hakan ne ya sa hankalin ‘yan uwa da abokan arziki ya tashi aka yi ta cigiya ba a same shi ba, cikin ikon Allah sai jami’an tsaro suka yi nasarar cafke motar da barayin a jihar Imo. Barayin suka yi bayani da ya kai ga samun gawarsa.

Kafin Rasuwan sa

Jaafar Manga direba ne mai neman na kansa wanda ya jajirce sai da taimakon Allah ya mallaki motar kansa wanda da ita yake aiki da suka karbe ta suka kashe shi.

Marigayin yana da mata biyu da yara biyar, yana Unguwar Wuro Birji a Bolari jihar Gombe.

Ubangiji Allah ya karbi Shahadar sa ya baiwa iyalai da ‘yan uwa hakuri kan wannan babban zalunci da aka yi musu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *