Tsohon Sarki Sanusi Zai Zo Kaduna Don Sauƙaƙa Wa Masu Kai Masa Ziyara A Legas

Tsohon Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II zai zo jihar Kaduna don sauƙaƙa wa masu kai masa ziyara a Legas.

Wata sanarwa da ta fito daga shafin Facebook na Sanusi II Dynasty, wadda wani, Murtadha Muhammad Gusau ya fitar ta bayyana cewa tsohon Sarkin na Kano zai zo Kaduna ranar Lahadi, 23 ga Agusta, 2020 zuwa Asabar, 29 ga Agusta, 2020.

“Ana sanar da ‘yan uwa masoya da magoya baya, da dukkanin masu fatan alkhairi ga Sarki Muhammadu Sanusi II cewa, duba da irin yadda mutane suke ta dawainiyar zuwa Birnin Lagos domin yin gaisuwa ga Sarki Muhammadu Sanusi II, kasancewar shi Sarki mutum ne mai tausayi, shine ya yanke shawarar zuwa Birnin Kaduna domin ya saukakawa masu son zuwa gaishe shi”, in ji sanarwar.

“Sanan kuma don Allah muna kira da a saka face masks (wato takunkumin fuska), kuma ayi kokarin bin dukkanin shawarwarin jami’an kiwon lafiya, saboda halin da ake ciki na jarabawar annoba da Allah ya kawo”, sanarwar ta ƙara da haka.

Leave a Reply

Your email address will not be published.