ZAFTARE ALBASHI: Duk ma’aikacin asibitin da ya ki zuwa aiki ya Kori Kansa – El-Rufai

 

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya gargadi ma’aikatan asibitocin jihar, da ya hada da nas-nas da likitoci cewa duk wanda ya biye wa kungiyar likitoci reshen jihar ya ki zuwa aiki, ya dauka tamkar ya yi sallama da aikin ne Kwata-kwata.

A takardar da gwamnatin jihar ta fitar ranar Alhamis wanda Muyiwa Adekeye ya saka wa hannu gwamna Nasir El-Rufai ya ce gwamnati ta na dukkan abinda ya Dace domin kula da ma’aikatanta.

” Kira da a fara yajin aiki a wannan yanayi na Korona, goga wa gwamnati kashin kaji ne kawai amma Babu dalilin yin hakan, inji shi.

” Duk ma’aikacin da yake son ya ci gaba da aiki da gwamnatin Kaduna ya je Inda yake aiki ya saka hannu a rajista.

” Wadanda kuma ba su son yin aikin kada su kuskura su ce za so datse kofofin asibitoci, ko wuraren kiwon lafiya. Ko kuma su ce za su muzantawa wadanda suka zo aiki. Yin haka karya doka ne.

” Ba ma’aikatan lafiya ba ne kawai aka zaftare musu Kashi 25 bisa 100 na albashin su, duka ma’aikatan gwamnati ne. Kuma su ba shafaffu da Mai bane da za a cire wa kowa amma a ki taba nasu albashin.

Gwamnati ta ce wannan Kashi 25 bisa 100 da ta zaftare a albashin ma’aikatan jihar kamar sadaka ne suka yi don tallafa wa talakawa da fakiran Kaduna da albinci a wannan lokaci da ake zaman gida dirshan babu ranar fita.

Bayan haka kuma, gwamnatin Kaduna ta ce ai su ma’aikatan lafiya ma ana biyan su alawus alawus a duk rana wasu ma’aikatan Naira 5000, wasu 10,000, wasu kuma 15,000, to Dan me zasu Tafi Yajin Aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: