Na Ɗauka Fyaɗe zai yi min, ban san cewa Yin Jima’i wajibi ne idan anyi aure Ba, Shi Yasa da Naji Wuya Kamar zai kashe ni na Burma mai Wuƙa.

BAN SAN IN AN YI AURE A NA JIMA’I BA

 

An kama wata budurwa Mai shekara 18 a duniya da laifin kashe mijinta Bayan ɗaura Musu Aure da Kwana 11 a lokacin da yaje zai kwanta da ita a Matsayin Matar sa.

 

Yarinyar mai suna Salma Hassan, wacce ke zaune a Itas-Gadau, Bayan kamata an kai ta ofishin ‘yan sanda a Bauchi a ranar Talata 19 ga watan Mayu.

 

Amaryar Ta bayyanawa manema labarai cewa lokacin da mijinta ya tinkare ta da niyyar zai kwanta da ita, tayi tunanin cewa abinda yake yi ba daidai bane, sai taki amincewa, tunda Ita ba ta Taɓa yin hakan ba kafin Yanzu.

 

Wannan Yasa mijin nata ya fara dukanta Saboda Taƙi Yarda ya kwanta da ita ta karfin tsiya. Ta ce sai ta dauki wuka da niyyar ta tsorata shi tsautsayi yasa ta caka mishi, inda ya ce ga Garin ku nan.

 

Ta ce: “Mun yi aure, muna son junan Mutuƙa.

 

A Daren da ya tinkaro ni da niyyar zai kwanta dani, sai naki amincewa saboda ban taba sanin wani abu jima’i ba, Nayi ta Roƙon sa cewa Yayi Haƙuri kada ya Mayar da ni ‘Yar Iska domin ni Ban Taɓa Iskanci ba, Inji ta.

 

“Sai yayi fushi, ya dinga marina da duka, yana kokarin kwanciya dani ta karfi, sai na dauki wuka domin na tsorata shi, amma sai ya cigaba da zuwa inda nake. Ban san lokacin dana caka masa wukar a kirji ba.

 

Bayan Mai Afkuwa ta Faru an kama ni sai na Fahimci Ashe Jima’i a Aure Wajibi ne kuma ta Haka Duk muka zo Duniya Yanzu haka Ina da Na Sanin Abin da na aikata kuma in na Tuna Baƙin Ciki ne ke Damuna.

 

A cewar ‘yan sanda sun samu wuka a lokacin da suka kama Salma Dan haka da Zarar mun Kammala Binkice zamu Gabatar da Ita Gaban Kotu, Inji su.

Leave a Reply

Your email address will not be published.