GWAMNATIN KANO: Ta kama motoci 45 wadan da suka bi barauniyar hanya domin shiga Kano daga Kaduna

GWAMNATIN KANO: Ta kama motoci 45 wadan da suka bi barauniyar hanya domin shiga Kano daga Kaduna ta Kwanar Dangora, tsakanin iyakar jihar Kano da Kaduna A Yau Alhamis.

Tuni Jami’an Gwamnatin jihar Kanon suka mika Tulin motocin a hannun kotun tafi da gidan ka karkashin shugabancin Salisu Idriss Sallama, inda daga bisani kotun ta daura musu tara yadda ya kamata.

Daga cikin motoci 45 din da jihar Kano ta kama, 30 daga Kaduna suka fito, 10 kuwa daga Jigawa yayin da sauran kuwa suka fito daga yankunan kasar daban-daban da niyar shiga birnin Kano.

A jawabin sa kan lamarin, Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya yaba da irin kokarin da Jami’an tsaro sukayi yana mai cewa su kara kokari ta hanyar karfafa sa’ido a dukkan wuraren da mutane ka iya shigowa jihar.

Ya kuma kara jan hankulan Jami’an tsaron da su himmatu sosai wajen dakile matsalolin garkuwa da mutane, fashi da sauran ayyukan ta’addanci tsakanin jihohin Kano da Kaduna.

“Ya kamata mutane su fahimci cewa wannan dokar da aka kafa anyi ta ne domin kare lafiyar al’uma baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.