Gwamnan Benue ya ce a Bude Masallatai da coci-coci kowa yayi Ibadar sa.

 

Gwamnatin jihar Benue ta bada umarnin ci gaba da ibada a coci-coci da Masallatan jihar inda tace kawai dai a riga yin Ibada da yawa fiye da da, saboda ba za’a bari mutane da yawa su rika shiga dakunan Ibadar a lokci guda ba kamar a baya.

Gwamnan ya Bayyana haka ne Jim kaɗan Bayan Fitowar su Daga Taron majalisar Ƙoli ta jihar daya gudana jiya Alhamis a grin Makurdi.

Sanarwar tace ma’aikata daga mataki na 1 zuwa 12 da aka ce su daina zuwa aiki zasu koma Bakin aikin su daga ranar 1 ga watan Yunin da Zamu Shiga, Inji shi.

Kazalika Dokar hana zirga-zirga tsakanin jihohi tananan sannan za’a ci gaba da amfani da dokar kulle da taƙaita Fita daga 8 na safe zuwa 6 na yamma.

Daga ƙarshe ma’aikatan zasu rika amfani da abin rufe hanci, Wanke Hannaye da kuma Bada Tazara Kamar Yadda Jami’an lafiya suka gindaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.