Wata Kotu Ta Yankewa Yunusa Yellow Hukuncin Shekara 26 A Gidan Yari

Wata babbar kotun tarayya dake zamanta a Yenagoa, babbar birnin jihar Bayelsa, ta yanke hukunci kan matashin nan dan asalin jihar Kano, wato Yunusa Yellow da ya dauki budurwarsa daga jiharta zuwa Kano.

 

Kotun ta zargi Yunusa Dahiru wanda aka fi sani da Inusa Yellow da zargin garkuwa da Ese Oruru daga gidansu a Bayelsa zuwa Kano tana ‘yar karamar yarinya sannan ya Musluntar da ita kuma ya aure ta.

 

Kotun karkashin jagoranicn Alkali Jane Inyang ta yankewa Yunusa Dahiru shekaru 26 a kurkuku kan laifuka biyar.

 

Idan ba a manta ba, an zargi Yunusa Yellow ya gudu da Ese tun a ranar 12 ga watan Agustan 2015, inda aka ce ya dauke ta a shagon mahaifiyarta dake birnin Yenagoa a jihar Bayelsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: