Rashin Zuwa Asibiti Ganin Likita Saboda Tsoron Cutar Corona Ne, Ya Janyo Yawan Mace Mace A Nigeria, Cewar Gwamnatin Tarayya

 

Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta ce tana fargabar akwai yiwuwar samun karuwar mace mace a kasar da ba su da alaka da coronavirus (COVID-19) tun bullar annobar a kasar.

Ta ce mafi yawancin mace macen suna faruwa ne saboda tsoro da wasu yan Najeriya ke yi na zuwa asibitoci inda za su samu kulawar da ta dace amma su ke kin zuwa don kada a gano suna da korona.

Ana kuma ganin cewa wasu daga cikin maaikatan lafiya suna kyashin duba marasa lafiya saboda tsoron kamuwa da cutar ta korona kamar yadda TheNation ta ruwaito.

Ministan Lafiya, Osagie Ehanire da ya bayyana hakan a yayin jawabin kwamitin kar ta kwana ta shugaban kasa kan COVID-19 a ranar Jumaa a Abuja ya ce adadin wadanda suke zuwa asibiti don awo, rigakafi da haihuwa duk sun ragu.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.