JAM’IYYAR PDP A KADUNA: Ta dakatar da Sanata Hunkuyi,John Danfulani da wasu mutane Biyar

Jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP a jihar Kaduna ta dakatar da Sanata Suleiman Uthman Hunkuyi da wasu jiga-jigan jam’iyyar mutum 6 a jihar sakamakon zarginsu da yiwa jam’iyya zagon kasa.

Kwamitin Gudanarwa na jam’iyyar PDP dake jihar kaduna, SWC, ya ba da sanarwar dakatarwar a ranar Asabar, bayan sauraron karar farko game da abunda ta kira da zagon kasa ga jam’iyyar.

Abraham Alberah Catoh, Sakataren yada labarai na Jam’iyyar PDP ne, ya shaidawa manema labarai cewa, SWC ta yanke shawarar dakatar da su kamar yadda kundin tsarin jam’iyyar ya tanada a sashe na 57 (3) 2017, (kamar yadda aka yiwa gyara)

A cewar sa wadanda aka dakatar sune Sen.

Suleiman Hunkuyi, Hon. Hashim Garba, karamar hukumar Kubau, Dr. Mato Dogara, karamar hukumar Lere, Ibrahim Lazuru, karamar hukumar Lere, Dr. John Danfulani, karamar hukumar Kachia, Lawal Imam Adamu, Karamar hukumar Soba, da Ubale Salmanduna daga karamar hukumar Zariya dake Kaduna jihar.

Ya ce “an dakatar da membobin ne daga jam’iyyar daga ranar 16 ga watan Mayu 2020 kuma ana sa ran za su bayyana a gaban kwamitin ladabtarwa a ranar da kuma lokacin da kwamitin zai sanar.”

kwamitin ya bayyana cewa Dauda Albehu Gora, ba halattan jam’iyya bane sojan gonane kamar yadda suka bayyana, sanna sun kara da cewa jam’iyyar ta mika sunan sa ga hukumomin tsaro domin lura da ayyukan sa, hakazalika ta kara dacewa zasu dauki matakin da ya dace muddin ya cigaba da ayyukan sa akan jam’iyyar PDP.

Leave a Reply

Your email address will not be published.