JAMI’AN TSARON NIJERIYA: Sun yi gagarumar nasara a jihohin Nasarawa da Benue, Sun kama wani Kasurgumin dan ta’adda

 

Hadin gwiwar jami’an tsaro karkashin Rundunar Operation whirl Strike a jihar Benue dana jihar Taraba sun kai samame a kauyen Mtan dake yakin Utenge na karamar hukumar Katsina-Ala dake jihar Benue inda nanne maboyar Kasurgumin dan ta’addarnan da ake nema Ruwa a Jallo watau Gana.

 

Samamen ya farune a jiya,Asabar, 16 ga watan Mayu inda aka kashe mutum 2 daga cikin yaran Gana din wasu kuma da dama suka tsere da raunukan bindiga.

 

Wasu Rahotanni da Hedikwatar tsaro ta samu sun bayyana cewa Gana ya tsallake rijiya da baya inda ya gudu da raunin bindiga a jikinsa.

 

Sanarwar Hedikwatar tsaron ta bayyana cewa ta kwato bindigu da harsasai da ababen hawa a Samamen.

 

Hakanan a jihar Nasarawa, Rundunar sojin ta yi nasarar kama wasu gungun mutane Kabilar Bassa dake shirin kaiwa kabilar Tibi hari saboda rashin jituwa akan rikicin Fili.

 

An kama mutanenne a Kpelebewa dake yankin Rukubi a karamar hukumar Doma dake jihar ta Nasarawa.

 

‘Yan kabilar Bassa 7 ne aka kama da tarin makamai da Layu da harsasai inda suke sanye da jajayen kaya. Ana bincike akansu kamun mikasu ga ‘yansanda.

Leave a Reply

Your email address will not be published.