Jami’an lafiya 24 ne suka kamu da cutar Korona Bairus a Jihar Bauchi 

 

Dr. Rilwanu Muhammad wanda shine shugaban hukumar lafiya ta matakin farko a jihar ne ya bayyana haka.

Ya bayyana hakane a wajan ganawa da manema labarai, sai dai yace babu wanda cutar ta kashe cikin jami’an lafiyar.

Yace wannan lamarin yasa jami’an lafiya a jihar kara dagewa wajan daukar matakan kariya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.