Duk Wanda Ba Ya Son Gwamna Masari Ni Ma Ba Na Son Shi, Saboda Masari Mutumin Kirki Ne, Cewar Sarkin Daura

 

Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar, ya bayyana cewa duk wanda bai son Gwamna Aminu Bello Masari, nima ban son shi. Saboda Gwamna Masari ke jajircewa wajen ganin al’umma jihar Katsina sun samu ingantanciyar lafiya, musamman a wannan lokaci na wannan annoba da ta addabi duniya.

Sarkin Daura ya bayyana haka ne, a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a gidansa da ke cikin rukunin gidaje na Barhim a cikin garin Katsina, bayan jinya da ya sha a asibitin kwararru ta Gwamnatin Tarayya da ke Katsina.

Sarkin Daura ya kara da cewa ” Gwamnatin jihar Katsina, karkashin jagorancin Gwamna Katsina, babu abinda ke gabanta sai kyautatawa talakka, shi yasa take kashe makudan kudade don su samu lafiya musamman lokacin wannan cuta mai hadari. Don haka ni ke kira ga talakkawa su zamanto masu biyayya ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamna Aminu Bello Masari. Dalilin wannan lalurar rashin lafiya tawa na gano Gwamnatin jihar Katsina na kashe makudan kudade kan talakkawa domin ceto rayuwarsu.

Mai Martaba Sarkin Daura Alhaji Umar Faruk Umar ya cigaba da cewa duk Wanda bai son Masari nima ba na son shi, saboda Masari mutumin kirki ne, Mai son talakkawa kuma gurin shi ya taimaka masu. Kuma tsayin daka ya kashe makudan kudi don ganin na samu lafiya. Saboda yadda na samu ingantanciyar lafiya tare da taimakon sa ne, a gaya mashi na samu lafiya.

Daga karshe Sarkin Daura Alhaji Umar Faruk Umar ya bayyana godiyarsa kan al’ummar kasar nan da na duniya ba ki daya kan yadda suka dukufa yi masa adduar a lokacin da ya ke kwance a asibiti. Haka kuma ya yi godiya ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari, kan kulawarsa da ya yi da ni, sau ukku yana rubuto wasika domin jajantawa da yake mani. Kuma Ina kira ga al’ummar kasar nan su cigaba da yin Addu’o’in ganin an samun sauki wanan annoba da ta addabi duniya. Kuma su zamanto masu biyayya da bin umurnin gwamnati.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.