CORONA VIRUS: An Ci Tarar Limaman Juma’a Guda Biyu Naira Dubu 20 A Jahar Bauchi Bayan Sun Jagoranci Sallah

Wata kotun tafi-da-gidanka a jihar Bauchi ta yanke wa wasu limamai biyu hukuncin biyan tara na naira 20,000 ko wanne, bayan ta same su da laifin jagorantar sallar Juma’a a masallatai daban-daban.

An gurfanar da limaman, Malam Musa Hassan da Malam Dahiru Alhaji, a gaban kotun ne ana tuhumar su da yin karan tsaye ga dokar gwamnatin jihar ta hana taruwa a wuraren ibada.

Duk su biyun dai a kauyen Dunkui Ambi na karamar hukumar Misau suke.

Alkali Abubakar ya yi kira ga al’ummar jihar su yi biyayya ga umarnin hukumomi.

A yanzu haka dai gwamnatin jihar ta Bauchi ta haramta tarukan jama’a, ciki har da taruka a wuraren ibada, a yunkurin hana kwayar cutar corona virus yaduwa.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.