Za Mu Bude Mutanen Jihar Katsina Su Yi Sallar Idi Da Bikin Hawan Sallah, Cewar Gwamna Masari

Duk da hauhawan da cutar Corona ke yi a jihar Katsina, Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya ce zaa dage dokar hana zirga zirga da gwamnatin jihar Katsina ta sanyawa wasu kananan hukumomin jihar Katsina da aka samu bullar annobar cutar Corona a cikin sati mai zuwa, domin al’umma su samu damar yin hidimomin saye-sayen kayan Sallah da yin Sallah idi da Kuma hawan Sallah a jihar Katsina na al’ada.

Gwamna Masari ya tabbatar da hakan a lokacin da yake wata hira ta musamman da manema labarai a Katsina.

Masari ya kara da cewa za mu sassafta wannan dokar domin ba al’umma damar yin sayayyar Sallah da hawan Sallah da Sallah idi da kuma Sallah idi a jihar Katsina a sati mai zuwa. Dagewar ba ta kwana daya ba ce ta kwanaki da dama ce.

Da ya juya kan matsalar tsaron da ta addabi wasu kananan hukumomi da suke fama da yan bindiga ya ce zuwa gobe za mu samu karin dakarun sojoji kasa a gobe asabar, sakamakon wata tattaunawa da muka yi da su a jiya. Harkar tsaro kacokan tana hannun Gwamnatin Tarayya , saboda sojojin da yan sanda duk hannunsu yake.

Masu Sharihi alammurran yau da kullum, sun bayyana cewa rufewar ba ta amfanawa jihar komai ba. Saboda cutar Corona dai kara karuwa take a jihar Katsina, a halin yanzu alkallumma sun nuna mutum sama da dari biyu ke dauke da ita. Kuma al’umma sun Shiga halin kunci musamman masu zuwa nema abinci. Mutane sun kara fadawa cikin taskon talauci, sakamakon kullen.

Leave a Reply

Your email address will not be published.