Gwamnatin Tarayya Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Kan Bude Masallatai Da Cocina

CORONA VIRUS: Gwamnatin Tarayya Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Kan Bude Masallatai Da Cocina Da Wasu Gwamnoni Suka Yi

 

Daga Aliyu El-Idrith Shu’aibu (Dan Autan Media)

 

A ranar Alhamis ne gwamnatocin jihohi hudu na Arewa suka sanar da bude masallatai da cocinan su. Jihohin sun hada da Borno, Gombe, Adamawa da Zamfara.

 

Matakin da Gwamnoni suka dauka ya sassauta dokar kulle don dakile yaduwar annobar corona a kasar nan.

 

Gwamnatin tarayya ta nuna rashin jin dadin ta a kan al’amarin kasancewar gwamnatocin jihohi ba su tuntube ta ba kafin sassauta dokar, kamar yadda The Nation ta rawaito.

 

Baya ga haka, gwamnatin tarayya ta yarda da cewa har yanzu yaduwar kwayar cutar na a matakin farko ne.

 

A daren jiya Alhamis ne NCDC ta tabbatar da cewa masu kwayar cutar corona virus sun wuce 5,000 a kasar na da mace-mace kusan 200.

 

Kwamitin yaki da cutar corona ta fadar shugaban kasa ta yanke hukuncin jin ta bakin gwamnonin.

 

Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya ce: “Muna tattaunawa da kungiyar gwamnonin Arewa. Mun san gwamnonin ba za su yi wani abu da zai jefa rayukan jama’arsu cikin garari ba tare da bata kokarin mu na makonni da suka wuce.”

 

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Yahaya ya ce za a bude wuraren bauta ne kadai inda za a dinga saka takunkumin fuska, kiyaye dokar nesa-nesa da juna da kuma wanke hannu akai-akai.

 

Yahaya yace za a horar da wakilan wuraren bauta don tabbatar da sun bi dokoki tare da kiyaye su.

 

Ya ja kunnen jama’a da kada su kuskura su take wata doka, don lamarin zai sa ya mayar da dokar hana zirga-zirga. Ba zai jure saka lafiyar jama’a cikin garari ba.

 

Gwamnatin jihar Adamawa ta dage dokar hana taron addinai a take.

 

Sakataren yada labarai na gwamna Fintiri, Hunwashi Wononsikou ya ce: “Gwamna Ahmadu Fintiri ya sassauta dokar hana zuwa bauta bayan saka dokar da yayi don dakile yaduwar cutar coronavirus.

 

“Ya bada umarnin bude masallatai, coci da kasauwannin Shanu da ke rufe.”

 

Gwamnatin jihar Borno ta sanar da dage dokar hana zirga-zirga har sai yadda ta kama.

 

Gwamnatin ta tabbatar da cewa za a iya taron addinai amma a kiyaye dokoki tare da amfani da takunkumin fuska.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: