Daga Salisu Magaji Fandalla’fih
Gwamnantin Najeriya ta ce bai zama wajibi a kanta ba ta bayyana inda likitocin China suka shiga – wadanda suka isa Najeriya a farkon bullar cutar Coronavirus – saboda ba ita ta gayyace su ba.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Ministan Lafiya Osagie Ehanire yana bayyana cewa likitocin na China ba baƙin gwamnnatin Najeriya ba ne domin kuwa sun shiga jasar ne da bizar kamfanin gine-gine na China Civil Engineering Construction Corporation (CCECC).
Ministan ya bayyana hakan ne jiya a wurin taron manema labarai na kullum kan matakan da ake dauka na yaƙi da cutar.
An yi ta ce-ce-ku-ce kan likitocin da suka iso Najeriya ranar 8 ga watan Afrilu sannan suka killace kansu na tsawon kwana 14 a wani wuri da ba a bayyana ba.
Ina tunanin ba dukansu ne likitoci ba, na ji cewa wasu daga cikinsu injiniyoyi ne kuma ma’aikatan kamfanin CCECC,” in ji ministan.
Ya kara da cewa: Ba Ma’aikatar Lafiya ce ta sauke su ba, saboda haka ba zai yiwu kodayaushe mu rika bayanin inda suke ba.
Waɗannan liktoci sun ja hankalin mutane da dama, amma ma’aikatan kamfani ne kuma da bizar kamfanin suka shigo.
Zan so ku daina tambayata a kansu domin ba bakinmu ba ne Sai dai mun koyi wasu abubuwa daga gare su kan abin da kasarasu ta yi game da yaku da cutar Coronavirus.”- inji Ministan na Lafiya.