Sanya Takunkumin Rufe Fuska Ya Zama Dole Ga Al’ummar Nijeriya, Inji Sakataran Gwamnati Boss Mustapha

A ranar Alhamis, 15 ga watan Mayu, gwamnatin tarayya ta ce a yanzu sanya takunkumin rufe fuska ya zama tilas ga dukkanin al’umma a fadin kasar nan.

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, shi ne ya sanar da hakan a ranar da ta gabata cikin babban birnin kasar na tarayya.

Mista Mustapha shi ne shugaban kwamitin da fadar shugaban kasa ta kafa domin lura da annobar korona a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.