Ta Kashe Mijinta Ta Hanyar Daba Masa Wuka A Kirji A Jihar Bauchi (Hoto Mai Razanarwa)

Lamarin da ya faru a yammancin jiya a garin Itas dake yankin Karamar hukumar Itas Gadau a jihar Bauchi, sabanin ya faru ne tsakanin ma’aurata guda biyu wanda ba su jima da yin aure ba. Sai dai majiyar tamu ba ta samu hakikanin sabanin da ya hada ma’auratan ba.

A yammancin jiya ne makotan ma’auratan suka jiyo hayaninya a gidan nasu isar su gidan ke da wuya suka tarar matar ta daba masa wuka a kahon zuciya har ya rasa ransa.

Tuni jami’an tsaro suka tasa keyar matar zuwa ofishin ‘yan sanda don zurfafa bincike akai.

Leave a Reply

Your email address will not be published.