Karya Ake Yi Min, Ina Kan Samun Sauki, Cewar Yaron Atiku Abubakar

Wasu sun kirkiri labari na karya suna yadawa game da lafiyar Muhammad Atiku Abubakar wanda Allah Ya jarrabe shi da cutar Corona virus .

Labarin yana cewa wai an kai Muhammad zuwa dakin agajin gaggawa na asibiti wato Intensive Care Unit (ICU) saboda wai rashin lafiyar ta yi tsanani a jikinsa.

Na ga labarin jiya da daddare, da safiyar yau ni Datti Assalafiy na yi magana da Muhammad din ta WhatsApp na masa forwarding labarin da ake yadawa a kanshi, ya tabbatar min da cewa karya ne, lafiyarsa kalau, baya jin wani ciwo a jikinsa, asali ma yana jiran sakamakon gwaji ne idan an tabbatar ya rabu da kwayoyin cutar za’a sallame shi nan da ba da jimawa ba.

Don haka labarin cewa Muhammad yana cikin mawuyacin hali bai inganta ba, kuma duk wanda ya ga labarin to ya yi watsi da shi.

Muna fatan Allah Ya karawa Muhammad lafiya tare da sauran ‘yan uwa Musulmai da suka kamu da cutar, kuma Allah Ya yayewa duniya wannan bala’i albarkacin watan Ramadan. Amin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *