KANO BATA RUFU BA!

Ra’ayina shi ne: lockdown ba hanya ce mai bullewa ba. Tunani na shi ne, wannan sigar ba zai fitar damu ba.

Zaka iya kulle kasashen Turai da wasu kasashen Latin Amurka da na Asiya, zasu iya daure kullewar, amma su ma ba zasu iya jure kullewa ba ta tsawon lokaci.

A Turai an gaya wa mutane su rufe komai ruf, kuma sun rufu, sun saba da bin doka, sun shaku da karbar umarni, suna kiyaye duk wani tsari. Banda mu a nan Africa, banda Najeriya, banda Kano.

Yau kwana biyu cibiyar da ke yin gwajin ta Kano ta tsaya cik. An daina gwajin. An saki kowa jiya ya yi warkajaminsa. Tun kuma da aka fara lockdown, mutane sallar Juma’a kawai suka daina a sahu-sahu komai normal yake tafiya.

A Lagos akwai guri 26 da ake daukar sample, tunda aka bude gwaji ba a dakata ba. A Lagos an basu kayan aiki, an basu kudi, kuma a tsaye suke. Duk jami’an lafiya basu da fargaba, isolation center da aka samar haufin da suke da shi kankani ne. A Oyo gwamna Seyi Makinde ya bada umarnin teloli su dinka takunkumi na mutum miliyan daya, wanda duk zai fita, ya daura ya rufe hanci da bakinsa, ya tafi harkarsa.

Mu bamu da magwaji, likitocin da malaman lafiyar basu da kayan kariya wato PPE, kayan gwajin ma babu, masu cutar kuma karuwa suke yi. Ga shi kuma an rufe mu ruf.

Wannan raguwar dabara ce. Kwana nawa zamu yi a rufe? Hutun kwana za a rika bamu a duk mako! Mutum nawa za a iya gwada wa a wata shida? Akwai wani adadi da ake so akai kansa, daga nan kuma magana ta kare?

Lockdown ba hikima bace, in hikima ce, to bata yi daidai damu ba, tafi karfinmu. Suma Turawa tafi karfinsu. Ba zamu iya ba. Allah ya sani ba zamu iya ba. A tsara mana wanda zamu iya. A Tanzania ba a yi lockdown ba. A Peru mata su fita yau da gobe maza su zauna a gida, jibi da gata su kuma su fita cikin shiri, A South Korea da Singapore da Taiwan rabawa biyu suka yi. Jihohi da yawa a Amurka sun ce zaman gida ya isa haka. A wasu kasashen kamar Norway da Finland sun ce ‘yan makaranta su koma. Muma a duba tamu mas’alar.

Duk masana lafiya har da Dr Tedros Ahmoud shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO sun ce za a iya daukar shekara biyu nan gaba wato zuwa 2022 sannan za a samu saukin Covid19. Zamu iya daurewa a haka?

Ku duba mana hanya ku samo mana dabara, zamu cutar da tattalin arzikinmu kuma ba zamu samu lafiyar da muke nema ba. A duba mana yanayinmu, a daukar mana mataki daidai yanayinmu da al’adarmu da kuma abin da zamu iya. Wannan lockdown ba zamu iya shi ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.