Gwamnan jihar Adamawa Amadu Umar Fintiri ya sake bada umurnin garkame jihar na wasu makonni biyu

Gwamnan ya bayyana hakan ne ta bakin Daraktan yada labaransa Solomon Kumamgar, a wata sanarwa da ya fitar a yau Juma’a a birnin Yola na jihar ta Adamawa.

Fintiri ya ce dokar garkame jihar zata fara aiki ne daga daren yau kuma zata kare ne a ranar 8 ga watan Mayu.

Gwamnan jihar ya ce baida wani mataki da zai iya dauka da ya wuce wannan a wani mataki na kare rayukan al’umma daga kamuwa da cutar da kuma dakile yaduwar cutar a jihar a daidai lokacin da aka samu mutum daya da yake dauke da cutar a jihar.

Sanarwar ta kara da cewa tuni gwamnatin ta kaddamar da shirin bibiyar mutanen da wanda ya kamu da cutar ya yi hulda da su, inda kuma za a yi wa wanda ya kamu maganin a wurin da ake killace da shi.

Fintiri ya roki al’ummar jihar da su ba su hadin kan da ya dace, inda ya ce duk da wahalar da ake sha, amma yin hakanne ya zama dole domin dakile yaduwar cutar.

Leave a Reply

Your email address will not be published.