Siyan Sarki: Sabon rikici ya balle tsakanin Gwamnatin Kano, Masarautar Kano da Nasiru Ado Bayero

Sarkin Kano da Sarkin Bichi

Rikici tsakanin Gwamnatin Kano da Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero ya balle bisa zargin ko halin ‘Ka karba daga gareni, kuma kaci min dunduniya.’

Majiyoyi daga cikin Masarautar Kano ta bayyanawa DABO FM cewa “Nasiru Ado Bayero yaki yarda da nadin da akayi masa na Sarkin Bichi bisa dalilai masu yawa’

Daga ciki akwai zargin “ya baiwa gwamnatin Kano, da wasu masu nema masa Sarki da uwargidan gwamnan na Kano kudade masu yawa da akayi masa alkawarin za’a bashi kujerar Sarkin Kano ba ta Bichi.”

Majiyar ta tabbatarwa da DABO FM cewar “Sarkin Bichi, Nasiru Ado Bayero yayi ikirarin yana da shaidun dukkanin kudaden da ya biya domin siyan Sarautar gidan DABO.”
Har ma yayi sharadin “Ko dai a biyashi kudin da ya kashe, ko a maida Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado, ya koma Bichi, shi kuma a bashi gidan Dabo.”

Haka zalika, majiyar ta tabbatarwa da DABO FM cewar akwai shirye-shirye da Masarautar Kano takeyi na tube rawanin wasu hakimai da masu mukamai ciki har da Sarautar Wazirin Kano.

DABO FM ta tattara cewar kafin rasuwar mai martaba Ado Bayero,ya nada limamin masallacin waje, Sheikh Muhammad Nasir Muhammad a matsayin Wazirin Kano wanda gwamnati bata amince da nadin ba.

Yanzu haka, majiyar ta tabbatar wa da DABO FM “akwai shirin dawo da wazirin mai murabus, Sheikh Muhammad Nasir Muhammad kan mukamin Wazirin Kano.”

Biyo bayan tsige wasu daga cikin manyan kujeru da suka hada da Makaman Kano da Sarkin Dawaki mai Tuta da sauransu wadanda akayi a sabbin masarautun da kananan hukumominsu suke, DABO FM ta tattara cewar sun cigaba da zuwa Masarautar Kano domin basu yadda dama da sabbin masarautun ba wanda majiyoyi suka bayyana Sarki mai murabus, Muhammadu Sunusi II ya cigaba da biyansu kudaden da ake basu.

Bisa dalilin haka ne majiyar tace masarautar Kano zatayi sabbin nadin wadannan mukamai bisa cewa “ba yan masarautar bane”, tare da yiwuwar sauke wasu hakimai daga kananan hukumomin da suke wakilta sakamakon umarnin gwamnan Ganduje na baiwa masu nadin Sarki kujerar hakimci a kananan hukumomi 4 dake karkashin masarautar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published.