‘Yan Majalissu guda 10 na jami’iyyar APC na jihar Kano sun bayyana cewar har yanzu suna nan daram a jami’iyyarsu ta APC kuma basu da shirin fita.
DABO FM ta tattara cewar anyi ta yada batun fitar yan majalissun daga APC zuwa PDP a shafukan sada zumunta musamman a Facebook daga wasu daga shafukan labarai.
Yan Majalissar sun bayyana matsayinsu na cewar suna nan a jami’iyyar APC ta bisa wakilcin dan majalissa Hon Labaran Abdul Madari Warawa mai wakiltar karamar hukumar Warawa.
Ya bayyana matsayar tasu ne yayin wata ganawa da yayi a shirin Hantsi na gidan Talabijin na Rahma TV a safiyar yau Talata.
“Wannan labarin yarfe ne kawai irin na siyasa, muna nan a jami’iyyarmu ta APC kuma babu inda zamuje.”
“Har yanzu da ko shekara daya bamuyi ba, muna nan zaune lafiya, bamu sabawa jami’iyya ko tsarinta ba, don haka muna nan a cikinta.
Haka zalika yayin karin haske game da rashin cigaba da bincikar gwamnan Kano, Dr Ganduje, kan batun zargin karbar dala da akan ga gwamnan yanayi a faifan bidiyo.
Hon Labaran Madara yace kotu ce ta yi umarnin dakatarwasu bisa dalilin cewar basu da hurumi a kan batun.