Dan Majalisar Tarayya Daga Sokoto Ya Kwashi Almajirai Zuwa Majalisa A Yayin Da Zai Gabatar Da Kudurin Gyara Da Inganta Almajiranci A Zauren Majalisa

Honarabul Balarabe Shehu Kakale matashi kuma sabon dan majalisa ya gayyaci al’ummar mazabar sa, domin su shaidi zaman majalisar wakilai ta kasa.

Da yammacin jiya tawagar Honarabul Balarabe Shehu Kakale Shuni suka bar filin jirgin saman kasa-da-kasa na Sarkin Musulmi Abubakar III dake Sakkwato domin karba goron gayyata na su shaidi zaman majalisar wakilai ta asa a gobe Alhamis inda Dan majalisar mai wakiltar mazabar BODINGA DANGE SHUNI da TURETA zai gabatar da muhawara akan inganta tsangayar Almajirai da Almajirci a Najeriya domin dogaro da Kai da samar da tsaro a Najeriya.

Wannan ne karon farko a tarihin siyasar wannan mazaba dake a jihar Sakkwato, da wani Dan majalisa ya dauki nauyin gayyato al’ummar mazabar sa, da wasu masana tare da masu ruwa da tsaki a kan sha’anin almajiranci a rayuwar su.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.