Da Tambuwal bai zarce ba da tuni shima Sarkin Musulmi da an tsige shi – Shehu Sani

Da Tambuwal bai zarce ba da tuni shima Sarkin Musulmi da an tsige shi – Shehu Sani

 

Tsohon dan majalisar tarayyya mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya ce idan ba don Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto ya lashe zabensa na zarcewa karo na biyu a kan mulki ba da an tsige Sarkin Musulmi kuma shugaban kwamitin kolin musulunci na kasa, Muhammad Sa’ad Abubakar II.

 

Shehu Sani ya yi wannan lafazin ne a lokacin da ya ke tsokaci a kan tsige tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II a ranar Litinin.

 

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje nan take ya amince da nadin Aminu Ado Bayero a matsayin sabon Sarkin Kano.

 

A cewar Shehu Sani a rubutun da ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta na Twitter, Idan ba domin Tambuwal ya yi nasarar sake cin zabe a matsayin gwamnan jihar Sokoto ba a babban zaben 2019 shima ‘shima sarkin musulmi da ke bayyana ra’ayoyinsa a kan abubuwan a ke faruwa a kasar da an tsige shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published.