ASUU Ta Tsunduma Yajin Aikin Gargaɗi

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i, ASUU ta tsunduma yajin aikin gargaɗi na makonni biyu daga ranar Litinin ɗin nan.

Shugaban ASUU na Ƙasa, Farfesa Biodun Ogunyemi ya sanar da haka a ƙarshen zaman Kwamitin Zartarwa na Kasa na ƙungiyar da aka yi a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Enugu, ESUST.

Farfesa Ogunyemi ya ce sun tafi yajin aikin ne don tilasta Gwamantin Tarayya ta aiwatar da Yarjejeniyar Aiwatarwa da aka tattauna a 2009 tsakanin ASUU da Gwamnatin Tarayya, Yarjejeniyar Aiwatarwa ta 2013 da Yarjejeniyar Aiwatarwa ta 2017, waɗanda duk ba a aiwatar da su ba.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *