Matasa A Kano Sun Ƙone Gidan Mahaifan Wani Mawaƙi Da Ya Yi Ɓatanci Ga Annabi

‘Yan sanda a jihar Kano na neman wani mawaƙi mai suna Yahaya Sharif-Aminu bisa zargin sa da yin wata waƙa ta ɓatanci ga Annabi Muhammad, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi.

 

Ɗaruruwan matasa ne suka bazu a kan tituna ranar Laraba, inda suke nuna fushi bisa wannan ɓatanci, suka kuma yi kira da a ɗauki mataki.

 

Majiyarmu ta ruwaito cewa wannan mawaƙi fanɗararren ɗan Tijjaniyya ne kuma ɗan Faira, wasu gungun mutane a Tijjaniyya waɗanda ke ƙetare iyaka wajen yabon Sheikh Ibrahim Inyass, shararren malamin addinin Muslunci ɗan Senegal.

 

Masu zanga-zangar sun yi tsinke a Hukumar Hisbah da yawansu don su bayyana fushinsu bisa wannan ɓatanci.

 

Waɗanda ke riƙe da kwalaye masu ɗauke da saƙonni daban-daban, matasan sun yi zargin cewa gwamnati da hukumomin tsaro a jihar ba sa son ɗaukar mataki a kan al’amarin, abinda ya tilasta su yi zanga-zanga don nuna fushinsu a kan ɓatancin.

 

Da yake jawabi ga manema labarai, jagoran masu zanga-zangar, Idris Ibrahim, wanda aka fi sani da Baba Idris, ya ce sun zo ne don su sanar da gwamnati don ta yi abinda ya dace, idan ba haka ba kuma za su ɗauki doka a hannunsu.

 

Ya ƙara da cewa irin haka ta faru a jihar a baya, amma batun ya shiririce ba tare da wani hukunci ba daga hukumomi jihar.

 

A ta bakinsa, a wannan lokaci ba za su bar ɓatancin ya wuce ba tare da yin hukunci ba.

 

Mista Sharif-Aminu ya yi wata waƙa ne inda ya yi baituka na ɓatanci ga Annabi Muhammad, abinda ya sa matasan Musulmi suka fustata.

 

Rahotonni suka ce da fusatattaun matasan suka kasa samun sa a gida, sai suka ƙona gidan iyayensa ƙurmus da yake unguwar Sharifai ta yankin ƙaramar hukumar Kano Municipal.

 

Da yake yi wa matasan masu zanga-zanga jawabi, Kwamandan Hisbah, Harun Ibn-Sina ya ce jami’ai a jihar suna aiki a kan al’amarin, yana mai cewa tuni an cafke iyayen mawaƙin, kuma suna hannun ‘yan sanda.

 

Shi ma da yake jawabi, wakilin Kwamishinan ‘Yan Sanda na Kano, CP Habu Sani, ya faɗa wa masu zanga-zangar cewa ‘yan sanda suna nan suna ƙoƙarin kama mawaƙin da ya gudu.

 

Wakilin na CP, wanda ya ce sunansa Hamza, ya yi kira ga masu zanga-zangar da su kasance masu bin doka ta hanyar ƙyale jami’an tsaro su yi abinda ya dace.

 

Ya tabbatar wa da cincirindon matasan cewa za a hukunta wannan mawaƙi.

Leave a Reply

Your email address will not be published.