Coronavirus: Masallatan Makka Da Madina Sun Kasance ‘Babu Kowa’

A ranar Laraba ne Saudiyya ta dakatar da ‘yan ƙasar da kuma ‘yan ƙasashen waje mazauna ƙasar zuwa Umara, a cewar Kamfanin Dillancin Labarai na Saudiyya.

 

Wasu hotuna da shafin Facebook na Haramain Sharifain ya wallafa sun nuna yadda masallatai masu tsarki guda biyu na Makka da Madina suka kasance babu kowa sakamako wankewa da zuba magani da ake yi.

 

A cewar wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta fitar, ta ce an ɗauki wannan matakin na hana ‘yan ƙasar da kuma ‘yan ƙasashen waje mazauna ƙasar zuwa Umarar ne ne bisa shawarar da wani kwamiti da aka kafa wanda zai riƙa bibiyar yadda Coronavirus, wadda aka sauya wa suna zuwa Covid19 ke ci gaba da yaɗuwa a ƙasar.

 

Hukumomin da abin ya shafa za su ci gaba da duba hukuncin, kuma za su iya janye hukuncin duk lokacin da suka ga cewa dalilan da suka sa aka dakatar da zuwa Umarar sun ɓata.

 

Idan dai za a iya tunawa, an samu rahoton ɓullar Covid19 ne a Saudiyya ranar Litinin.

 

Ma’aikatar Lafiya ta sanar da ɓullar Coronavirus ta farko a ƙasar wadda wani ɗan ƙasar da ya dawo daga Iran ya shigar ƙasar.

 

A matsayin wani ɓangare na ɗaukar matakan kariya, Ma’aikatar Harkokin Ƙasashen Ƙetare ta dakatar da bayar da bizar Umara ga dukkan ƙasashen duniya, haka kuma ta dakatar da zuwa yawan buɗe ido ga wasu ƙasashe 22, matakin da ya fara aiki tun ranar Alhamis da ta gabata.

 

Amma hukumomi sun yi bayanin cewa wannan hani bai shafi fasinjoji da suke riƙe da bizar aiki ba, bizar ziyarar aiki, bizar ziyarar kasuwanci da kuma bizar ziyarar iyali.

 

A ranar Talata, Majalisar Ministoci ta jaddada cewa an ɗauki matakan kariyar ne don tabbatar da tsaron lafiyar ‘yan ƙasar, ‘yan ƙasashen waje, alhazai da kuma masu ziyara.

 

“An ɗauki waɗannan matakan ne don a tallafi ƙoƙarin tabbatar da isasshiyar kariya ga ‘yan ƙasa, mazauna Saudiyya da kuma dukkan waɗanda za su zo ƙasar don yin Umara, ziyarar Masallacin Annabi ko kuma don yawon buɗe ido”, Majalisar Ministocin ta bayyana haka a cikin wata sanarwa.

 

Majalisar ta kuma yaba da ƙoƙarin da Ma’aikatar Lafiya tare da haɗin kan Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida da Ma’aikatar Tsaro da sauran hukumomin gwamnati don shawo kan cutar da kuma bibiyar yadda cutar ke shafar tattalin arziƙi, tare da ɗaukar matakan da suka wajaba don shawo kan cutar.

Leave a Reply

Your email address will not be published.