Gwamna Nasiru El-rufai Ya Kai Ziyarar Ta’aziyya Masarautar Kano

Gwamna jihar Kaduna Malam Nasiru El-rufai ya kaiwa mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ziyarar ta’aziyyar rashin Kawunsa Ambassada Ado Sanusi I (Dan Iyan Kano, Murabus), da kuma Gwaggonsa Hajia Hauwa Sanusi Bayero, wacce ta rasu a daren jiya.

A makon jiya ne dai Allah ya yiwa Jakada Ado Sanusi I rasuwa bayan ya yi fama da jinya.

A lokacin rayuwarsa dai ya taba zama jakadan Najeriya a kasashen, Saudiyya da Iran da Morocco da kuma jamhuriyar Musulunci ta Iran.

A karshe Gwamna El-rufai ya yi addu’ar Allah ya ji kansu da gafara, tare kyautata namu zuwan.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.