Yadda ‘Yan Bindiga Suka Kashe Mutane Sama Da Hamsin A Kaduna

 

A ranar Lahadi, wasu ‘yan bindiga sun kai hari a wasu kauyuka dake karkashin karamar hukumar Igabi ta Jahar Kaduna.

Kauyukan da abin ya shafa sun hada da , Zareyawa, Marina dake gundumar Kerawa inda suka hallaka mutane 51 suka jikkata wasu sannan suka kone motoci da dama.

Majiyarmu ta shaida mana cewar maharan sun kai samamen ne da Asuba musalin karfe 6:00 ana idar da sallar Asuba.

Inside Arewa Hausa ta sami rahoton cewar mafi yawan ‘yan kauyukan sun gudu yayin da maharan suka kona gidaje da dama sannan suka yi awon gaba da kayan masarufi (abinci).

Kansilan gundugumar Kerawa, Malam Dayyabu Kerawa ya tabbatarda aukuwar lamarin ga wakilin Daily Trust kuma ya kara da cewa an burne mutum 51 da suka rasa rayukansu da misalin karfe 4 : 00 ma yamma.

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.