MAZA GUMBAR DUTSE: Ba Zan Yi Sulhu Da ‘Yan Ta’adda Ba, Kuma Na Daura Damarar Kawo Karshensu A Kaduna, Cewar Gwamna Elrufai

MAZA GUMBAR DUTSE: Ba Zan Yi Sulhu Da ‘Yan Ta’adda Ba, Kuma Na Daura Damarar Kawo Karshensu A Kaduna, Cewar Gwamna Elrufai

“Na rantse da girman Allah ba zan tausayawa mutanen dake kashe al’umma haka kawai ba, zan tabbatar musu da cewa Nine Nasiru mai rusau, za su yabawa aya zakinta, za su fuskanci fushi, kuma cikekken fushi daga shugaban dake kishin mutanensa.

Rashin mutumcin naku ya yi yawa, baku san ya kamata ba, baku san daidai ba, yadda kuke kashewa ba tare da tausayi ba, haka za mu zazzaga muku ruwan bala’i za mu ragargaje ku, za mu dauki fansa ba tare da sassauci ba.

Ku kashe mutane sama da hamsin, haka kawai ba tare da sun aikata muku kowanne irin laifi ba. Za ku gane cewa Gwamnati ba wasa ba ce”, cewar Gwamna Elrufai.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.