Ku Kwantar Da Hankalinku, Kada Ku Tsorata Da Cutar Corona Virus, Shugaba Buhari Ga ‘Yan Nijeriya

 

Fadar Shugaba Muhammadu Buhari ta fitar da sanarwa cewa, ya yi kira ga kowa ya kwantar da hankalin sa, dangane da bullar cutar Coronavirus.

PREMIUM TIMES ta ruwaito labarin bullar cutar a karon farko a Lagos, bayan da wani Baturen kasar Italiya ya shigo cikin kasar nan dauke da cutar.

Tun bayan killace shi da aka yi a Lagos da sauran jihohi da dama suka fara daukar kwararan matakan yin kaffa-kaffa, ta hanyar wayar da kan jama’a dangane da matakan kariya ko gujewa ga kamuwa da cutar.

An kuma bada labarin killace wasu ‘yan China su uku, a jihar Filato, tare da wasu ‘yan Najeriya su 39 da ke wa ‘yan Chana din aikin hakar ma’adinai.

A jihar Cross River gwamnatin jihar ta dukufa wajen yin amfani da shela da kuma cikin coci-coci ta na fadakar da jama’a cikin yare daban-daban.

Cikin sanarwar da Garba Shehu yayi, Kakakin Yada Labarai na Buhari ya fitar, Buhari ya ce ‘yan Najeriya su daina tsorita, domin yawan tsoritar zai iya yi wa Najeriya mummunan illa.

Buhari ya nuna jimamin yadda aka samu wani mutum da ya shigo da cutar, duk kuwa da irin karfafan matakan da aka dauka domin guje wa hakan.

Ya kuma gode wa hukumomin lafiya na kasa, musamman na Jihar Lagos da na Jihar Ogun, dangane da kokarin gaggawa da suka dauka wajen gano mai dauke da cutar.

Daga nan ya ce a daina tsorita, maimakon haka, kowa ya rika kiyayewa da matakan kariya da na kaucewa daga kamuwa, wadanda ake ta sanarwar su a kafafen yada labarai.

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.