Hukumar EFCC Ba Ta Da Hurumin Kwacemin Kadarorin Da Na Mallaka, Cewar Sanata Bokola Saraki

 

Tsohon shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki, ya bukaci babbar kotun tarayya da ke Legas, ta yi watsi da bukatar da hukumar EFCC ta kawo gabanta.

Bukola Saraki, ya bukaci kotu ta yi watsi da karar da EFCC ta kawo inda ta ke bukatar a karbe gidansa da ke Garin Ilorin a jihar Kwara, a dankawa gwamnatin tarayya.

Bukola Saraki ya fadawa kotu cewa bai kamata ta yi amfani da jita-jitar jama’a da ke cewa, an gina wadannan gidaje da dukiyar haramun wajen karbe masa dukiyarsa ba.

Lauyan da ya ke tsayawa Abubakar Bukola Saraki, wato Kehinde Ogunwumiju SAN, ya roki kotu ta bukaci Jami’an EFCC su kawo hujjar da ke gaskata zargin da ta ke yi masa.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *