Muna Bukatar Karin Sojoji Dubu Dari Domin Cin Galaba Akan ‘Yan Boko Haram, Cewar Gwamna Zulum

Muna Bukatar Karin Sojoji Dubu Dari Domin Cin Galaba Akan ‘Yan Boko Haram, Cewar Gwamna Zulum

 

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya ce Nijeriya na bukatar karin sojoji 100,000 domin cin galaba a kan ‘yan Boko Haram.

 

Ya bayar da shawarar cewa a dauki a kalla mutane 50,000 aikin soja daga jihar Borno domin su tallafa wurin yaki da ta’addancin ko suna da karatun boko ko ba su da shi.

 

Zulum ya yi wannan jawabin ne yayin da ya karbi bakuncin tawagar kwamitin tsaro na majalisar wakilan tarayya a ranar Laraba karkashin jagorancin Hon. Babajimi Benson.

 

Gwamnan ya jadadda cewa ba za a iya cin nasara a yaki da ‘yan ta’addan ba sai an samu isasun sojoji da fasaha da kudi.

 

Zulum ya shaidawa Benson yayin ziyarar sa cewa “ba za ka iya kawo karshen ta’addanci ba idan ba ka da makamai da fasahar zamani da isasun kudi.”

 

Ya ce, “Rundunar soji ba ta da isasun dakaru, ba su da kayan aiki.

 

Ku shawarci Kakakin majalisa da Shugaban Majalisar Dattawa su fada wa Shugaban kasa ya bayar da umurnin daukan sabbin sojoji. Mu na bukatar a kalla sojoji 100,000.

 

Su zo su dauki ‘yan asalin jihar Borno aikin soja ko suna da karatun boko ko ba su da shi.

 

“Muna bukatar daukan a kalla mutane 50,000 daga Borno, muna da jaruman maza da za su iya shiga aikin soja ko da na wucin gadi ne.”

Leave a Reply

Your email address will not be published.