Kwankwaso Ya Nemi A Sake Duba Hukuncin Shari’ar Zaben Gwamnan Kano A Kotun Koli

Kwankwaso Ya Nemi A Sake Duba Hukuncin Shari’ar Zaben Gwamnan Kano A Kotun Koli

 

Tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabiu Musa kwankwaso Ya Nemi Goyon Bayan Shugabannin Jam’iyyar PDP Na Kasa Domin Duba Hukuncin Gwamnan Kano A Kotun Koli.

Sanata Kwankwaso Tare Da Dan Takarar Gwamna Na PDP, Abba K. Yusuf Da Sauran Manyan Masu Ruwa Da Tsaki Na PDP Daga Jihar Kano Sun Kai Ziyara Babban Ofishin Jam’iyya Na Kasa Dake Abuja

Kwankwaso Ya yi Kira Ga Kwamitin Na Kasa Daxsu Dauki Nauyin Sake Duba Hukuncin Da Kotun Koli Ta yi kan zaben Kano.

Da Yake Mayar Da Martani, Shugaban Jam’iyyar Na Kasa Prince Uche Secondus, wanda ya samu Wakilcin Mataimakinsa Sanata Suleiman Nazif Yace PDP Ta Dauki Kano A Matsayin Babbar Cibiyar Siyasa A arewacin Najeriya Kuma Zata Yi Duk Abinda Doka Ta Tanada Don Kare Muradun jam’iyyar A jihar.

Sanata Nazif Ya Yabawa Kwankwaso Saboda kokarinsa Na Jagorantar Jam’iyyar Inda Har Aka yi Nasara a Zaben Gwamna Na Shekarar 2019.

Sanata Nazif Ya Tabbatar Wa Da Tawagar Da Suka Kawo Ziyarar Cewa Bukatar Gabatar Da Kara A Kotun Koli kuma Za’a Gabatar A Gaban kwamitin Da Yake Da Alhakin Aikin A Ofishi Uwar Jama’ar Ta PDP Dake Abuja yace Don Amincewa, “Ina Ganin Sakamako Mai kyau kan wannan bukatar saboda a bayyane yake cewa PDP Taci Zabe A Kano” .

A Rawaito cewa za a gabatar da bukatar gaban kotun kolin ne domin kotun ta sake duba hukuncin da ta yi kan shari’ar ta Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published.