Rikici a fadan Shugaban kasa Monguno yace Abba kyari ne ke bada Umarni ma Rundunar Sojojin Nijeriya

Rikici a fadan Shugaban kasa Monguno yace Abba kyari ne ke bada Umarni ma Rundunar Sojojin Nijeriya ba tare da Sanin Buhari ba.

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaron kasa Babagana Monguna, ya zargi Shugaban Ma’aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari da yi wa harkokin tsaron kasa katsalandan da saka baki a abubuwan da ba shi da iko akai.

A dalilin haka Mongonu ya aika wa manyan hafsoshin Najeriya dake shugabantan rundunonin tsaro na sojoji da wasikar gargadi cewa kada su kuskura su rika karbar umarni daga Abba Kyari daga yanzu.

” Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa ba ya cikin jerin masu iya zartar da wata doka a kasar nan sannan bai yi rantsuwa don kare kasa Najeriya ba saboda haka babu dalilin da zai sa ya rika cusa baki a harkokin kasa ba.” Inji Janar Monguno.

” A dalilin haka bai kamata sannan sabawa doka ce ya rika ganawa da ta musamman da manyan hafsoshin Najeriya da shugabannin tsaron kasa ba, jakadun kasashen waje ba tare da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro da ministocin da ya kamata su na tare a zaman ba. Yin haka saba wa dokar kasa ce.

” Ire-iren wadannan zumudi, da cusa kansa a binda ba huruminsa bane da nuna isa da ba da umarni ba tare da Buhari ya sani ba da Kyari ya ke yi, suna kawo mana cikas a ayyukan samar da tsaro a kasa Najeriya da kuma koma baya da ake samu wajen tabbatar da samun nasara a ayyukan da shugaba Buhari ya sa a gaba.

Wannan wasika na Monguna ya zo ne a daidai matsalar tsaro ya dawo danye a kasar nan sanan ‘yan Najeriya na kuka akai matuka.

Daga Bappah Abubakar

Leave a Reply

Your email address will not be published.