Buhari ba zai sallami shugabannin tsaro ba – Boss Mustapah

Buhari ba zai sallami shugabannin tsaro ba – Boss Mustapah

Daga Salisu Magaji Fandalla’fih

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai salami shugabannin tsaro ba.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa sakataren gawmnatin ya sanar da hakan ne yayin zantawa da manema labarai a Abuja a Yau Talata.

Mustapha ya ce lokacin sauke shugabannin tsaron bai yi ba saboda karuwar rashin tsaron a
kasar nan.

Ya ce halin da kasar nan take ciki tana bukatar “taimakon kowa”.

Leave a Reply

Your email address will not be published.