An Zargi ‘Yan Sanda Da Yin Fashi A Garin Dambam Dake Jihar Bauchi

An Zargi ‘Yan Sanda Da Yin Fashi A Garin Dambam Dake Jihar Bauchi

 

Daga Bala Muhammad Dambam

 

Jiya an yi fashi da makami a garin karamar hukumar Dambam dake jihar Bauchi, to amma bayan ‘yan fashin sun hada cunkoson motoci (gosulo), direbobi suka yi kukan kura suka tunkaro ‘yan fashin, nan take aka yi sa’a suka tsere suka bar motarsu tare da harsashai da wayar salula guda.

 

Abin mamaki kayayyakin baki daya na jami’an ‘yan sandan yankin Dambam ne, inda a ciikin daren direbobi da fasinjoji suka kawo kayayyakin fadar Dambam.

 

To yanzu abin jira a gani shine mu ji yadda za ta kaya tsakanin DPO na ‘yan sanda da hukumomi.

Leave a Reply

Your email address will not be published.