Na Kashe Mijina Ne Sakamakon Rikicin Sanya Cajin Waya, Cewar Rabi Rabi’u

Daga Jamilu Dabawa, Katsina

A ranar 29/1/2020, Rabi Rabi’u yar shekara goma sha bakwai da haihuwa da ke garin Almakiyaya, da ke karamar hukumar Malumfashi a jihar Katsina ta kashe mijinta Shamsu Salisu dan shekara ashirin da biyar da haihuwa har lahira sakamakon sabanin da suka samu na cazar wayar hannu, inda ta burma ma shi wuka a cikinsa.

Rabi ta bayyana haka a helkwatar rundunar yan sanda ta jihar Katsina, a lokacin da ta ke hira da manema labarai. Inda ta ce a wannan rana “gabanin sallah asuba ne na taso zan sanya caji an maido wuta, sai ya ce shi zai sa, na ce ya yi hakuri amma ya ki yadda” in ji ta.

Malama Rabi ta kara da cewa “tun ranar lahadi ya ke ta jin haushi na, sai ya yi ta zagina yana cewa na yi mashi laifi, na zo zan kwanta sai na ga ya dauko wuka, ni kuma sai na rike wukar muka kama kokawa a cikin dakin, har na samu nasarar amshe wukar na soka masa ita a ciki”

Cikin kuka da kaduwar da na sani Rabi ta ce duka-duka kwanan mu hamsin da daya da wannan auren da na yi da mijina Shamsu kuma ba auren dole ba ne aka yi man, Ina son shi yana sona.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.