Hukumar Kwastam Ta Nigeria ( NCS ) Ta Fitar Da Sunayen Mutum 162,399 Domin Rubuta Jarabawar Aptitude Test

 

Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) ta ce ta fitar da sunayen masu neman shiga aikin mutum 162,399 wadanda za su rubuta Jarrabawar cikin Mutum 828,333 da suka nemi shiga aikin a shekarar 2019.

A watan Afrilun shekarar 2019 ne Ma’aikatar ta fara shirin daukan ma’aikata guda 3,200.

Sanarwar ta fito daga bakin PRO, Mataimakin Kwamishina Joseph Attah a ranar Litinin ya ce an kalubalanci daukar ma’aikatan ne ta hanyar masu yaudarar wasu suna amfani da intanet na karya.

“Babban kwamandan kwastam din, Kanar Hameed Ibrahim Ali (Rtd) ya nuna takaici game da ayyukan masu aikata wadannan abubuwan, ya kuma ba da tabbacin jajircewar sa na shugabantar da tsarin daukar ma’aikata wanda zai zama abin gaskiya, a bayyane kuma mai sauki daga farko.

Sanarwar ta ce. ‘yan takarar da aka zaba domin yin jarabar sun sanar da su ta adireshin Emai da lambobin waya.

“Saboda haka, duk wadanda aka sanar za su yi gwajin kwarewar su a cibiyar da aka turo musu su kiyaye wajan.

“Don kaucewa shakku, tsarin daukar ma’aikatan na NCS KYAUTA ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *