An Kwantar Da Gwamnan Bauchi A Asibiti

 

An kwantar da gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed (Kauran-Bauchi) a wani asibiti can a kasar Landan.

Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban mataimaki na musanman ga gwamnan jihar ta Bauchi akan harkokin yada labarai, Mukhtar Gidado kuma aka raba ta ga manema labarai.

Inda kuma daga can gadon asibitin gwamnan dake kasar Landan ya aiko da sako na musanman ga al’ummar jihar Bauchi cewa yana shaida masu yanzu haka yana kwance a gadon asibitin ana dab da saurarar hukuncin karar sa da aka yi a gaban kotun daukaka kara.

Leave a Reply

Your email address will not be published.