Hurumin Sakin Sheikh Zakzaky Na Hannun Gwamna Elrufai, Cewar Gwamnatin Tarayya 

 

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa gwamnatin jihar Kaduna a karkashin jagorancin Malam Nasir Ahmad El-Rufai ce kadai za ta iya sakin shugaban kungiyar yan Shia ta yan uwa Musulmi, Sheikh Ibrahim Zakzaky.

 

Jaridar The Nation ta ruwaito ministan sharia, kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami ne ya bayyana haka a ranar Alhamis, 27 ga watan Disamba, inda yace ana tuhumar Zakzaky a karkashin dokokin jahar Kaduna ne ba dokokin tarayya ba.

 

Malami yace sharia’ar Zakzaky ba daidai take a shari’ar Sambo Dasuki da Omoyele Sowore ba, mutane biyun da gwamnatin tarayya ta sake su a ranar Talata, 24 ga watan Disamba bayan kwashe tsawon lokaci a hannu.

 

“Idan har ana tuhumar wanda ake zargi da aikata laifi a karkashin dokokin jaha ne, toh umarnin kotu na bayar da belinsa ya rataya ne a kan gwmanatin jaha, haka zalika idan ana tuhumar wanda ake zargi da aikata laifi a karkashin dokokin gwamnatin tarayya ne, umarnin kotu na bayar da belinsa na kan gwamnatin tarayya.” Inji shi.

 

Idan za’a tuna, Zakzaky da matarsa Zeenah sun shiga hannu ne tun bayan arangama da aka yi da Sojoji da yan Shia a wata Disamba na shekarar 2015 yayin da yan Shian suka tare ma babban hafsan sojan kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai hanya a garin Zaria.

 

Sai dai duk umarnin da wata kotu ta bayar a watan Disambar 2016 na sakin Zakzaky da matarsa, gwamnati ta ki sakinsa, inda a ranar 18 ga watan Afrilun 2018 gwamnatin jahar Kaduna ta maka shi gaban kotu tana tuhumarsu a kan laifuka 8.

Leave a Reply

Your email address will not be published.